Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Katafariyar Kasuwar Zamani Ta Shoprite Ta Sanya Ranar Barin Kano

Kamfanin Kasuwar Shoprite ya yanke shawarar bin kamfanin Procter & Gamble da sauran manyan kamfanonin ƙasa da ƙasa na dakatar da kasuwanci a reshensa na Kano daga ranar 14 ga watan Janairu mai kamawa.

A sanarwar da kamfanin Shoprite ya saki ranar Alhamis, ya ɗora laifin barin Kanon ne kan wahalhalun kuɗaɗe da tsadar samar da kayayyaki da kamfanonin kasuwanci ke fuskanta a Najeriya.

Wannan na zuwa ne bayan sanarawar da kamfanin Jumia Food ya fitar ta dakatar da aiyukansa a Najeriya a ƙarshen wannan watan saboda yawaitar matsalolin tattalin arziƙin da ake fuskanta a ƙasar.

Kamfanin Shoprite ya sanar da takaicin bayar da sanarwar dakatar da aiyukansa a Kano, inda ya bayyana hakan a matsayin mataki na dole, ya kuma ce aikin da ma’aikatan kasuwar suke yi zai zo ƙarshe da zarar an dakatar da kasuwar.

Baya da Shoprite, kamfanoni irinsu Procter & Gamble da GlaxoSmithKline Consumer Nigeria Plc sun sanar da dakatar da aiyukansu saboda matsin tattalin arziƙin da ake fama da shi a ƙasa.

Da take magantuwa kan lamarin, Ƙungiyar Masu Samar da Kayayyaki ta Najeriya, MAN, ta bayyana cewar kamfanoni da dama zasu bar Najeriya saboda matsin tattalin arziƙin da ake fama da shi a Najeriya.