Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ƴansanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane A Kaduna

Rundunar Ƴansanda Reshen Jihar Kaduna ta kama wani mai suna Bello Muhammad mai shekaru 28 ɗan asalin Jihar Zamfara da ake zargi da yin garkuwa da mutane tare da ƙwato naira miliyan 2 da ake zargin ya karɓa ne daga iyalan waɗanda yake garkuwa da su.

Mai magana da yawun ƴansandan Jihar Kaduna, Mansir Hassan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya saki jiya a Kaduna.

Ya bayyana cewar, ƴansandan da ke Ofishin Ƴansanda na Yankin Tafa a Kaduna ne suka kama wanda ake zargin tare da karɓo wasu daga kuɗaɗen fansar da yake karɓa.

WANI LABARIN: Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Ɗaurin Shekaru 5 Kan Farouk Lawan

Mansir ya bayyana cewar, wanda ake zargin ya yi yunƙurin bayar da cin hancin naira miliyan 1 ga DPO na yankin domin ya kuɓutar da kansa amma bai samu nasara ba.

An dai kama wanda ake zargin ne a ranar 19 ga watan nan na Janairu da misalin ƙarfe goma na dare a wani otal mai suna Easyway Hotel da ke Tafa a Jihar Kaduna.

Mai magana da yawun ƴansandan ya bayyana cewar, Bello Muhammad ya amsa laifinsa a matsayin mai yin garkuwa da mutane a yankin dajin Kagarko da ke Kaduna.