Kwamitin Aiyyukan Haɗinguiwa na Ƙungiyoyin Matasan Arewa ya yi kira da a cire Ministan Kula Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo da gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Yemi Cadoso saboda shirinsu na mayar da ofisoshin ma’aikatunsu Lagos.
Wata takardar bayan taro da gungun matasan ya fitar a jiya Alhamis wadda jagoran tafiyar Murtala Abubakar ya sanya wa hannu tare da Daraktan Yaɗa Labarai, Hashim Tom Maiyashi da Daraktar Mata, Latifa Abdussalam, sun yabawa sanatocin Arewa tare da buƙatar sanatocin su buƙaci Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sauƙe mutane biyun.
WANI LABARIN: Ƴansanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane A Kaduna
Gungun matasan na Arewa sun nuna rashin goyon bayansu ga yunƙurin kai shugaban ƙasa kotu, sai dai sun buƙaci ƴan-majalissar da su bai wa shugaban wa’adi na tsayar da canza matsugunnin ofisoshin.
Matasan sun ƙara da cewar, duk wani hukunci da zai shafi tattalin arziƙin ƙasa da gudanar da gwamnati ya kamata ya zama a kan tsarin daidai, gaskiya da kuma biyayya ga kundin tsarin mulki.