Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ƴanbindiga Sun Kashe Ƴansanda Biyu A Enugu

A jiya Juma’a da daddare ne wasu ƴanbindiga suka kashe ƴansanda biyu da ke Rundunar Ƴansanda ta Jihar Enugu.

Ƴansandan da ke aiki ƙarƙashin Ofishin Yankin Ogui an ce suna kan aikinsu ne na binciken ababen hawa a kan titin Presidential Road da ke Enugu lokacin da suka fuskanci harin ƴanbindigar.

An rawaito cewar harin ya faru ne wajejen ƙarfe 9:30 na dare.

Da yake mayar da martani kan kisan da aka yi wa ƴansandan a yau Asabar, Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah ya sanya ladan naira miliyan goma ga duk wanda ya kawo ƴanbindigar.

Mbah ya ce, gwamnatinsa zata nemi masu laifin da duk ƙarfin da take da shi tare da tabbatar da cewar an hukunta su daidai da laifukansu.

Ya yi wannan alƙawari ne lokacin da yake jawabi ga manema labarai bayan zaman Kwamitin Tsaro na Jihar wanda ya samu halartar Kwamishinan Ƴansanda na jihar, Mr. Kanayo Uzuegbu; Daraktar Jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya a Jihar, State Director, Theresa Egbunu; Kwamandan Sojoji na Runduna ta 82, Brigadier General Murtala Abu; da Kwamandan Rundunar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi a Jihar, Peter Ogar, da sauransu.