Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Gwamnatin Tarayya Ta Bayar Da Hutun Ranar Demokaraɗiyya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana ranar Laraba, 12 ga watan Yuni, 2024 a matsayin ranar hutu a Najeriya domin murnar zagayowar ranar demokaraɗiyya.

A wata sanarwa da ta fita yau Talata daga Ministan Harkokin Cikin Gida, Tunji Ojo a madadin Gwamnatin Tarayya, ministan ya taya ƴan Najeriya murnar zagayowar ranar.

Ya ce, a lokacin da ƴan Najeriya ke murnar zagayowar wannan rana, akwai buƙatar kwaikwayon ƙoƙarin da mutanen farko a Najeriya suka yi tare da tabbatar da haɗin kai, tsaro da zaman lafiya.

Ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya da su zama masu bin tsarin demokaraɗiyya sau da ƙafa.

Tunji Ojo ya kuma bayyana cewar Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta mai da hankali wajen ganin ta farfaɗo da tattalin arziƙin Najeriya tare da samar da tsaro.