Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ganduje Da Matarsa Zasu Bayyana Gaban Kotu Gobe Alhamis Kan Zargin Cinhanci

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Ganduje da matarsa Hafsat da kuma waɗansu mutane guda shida zasu gurfana a gaban kotu a gobe Alhamsi domin su fuskanci zargin aikata aiyukan da ke da alaƙa da cinhanci, karkatar da kuɗaɗe da kuma yin almundahanar da suka kai na biliyoyin nairori.

Wannan dai na zuwa ne biyo bayan takardar sanarwar zaman sauraron ƙarar da kotu ta aike wa waɗanda ake zargin.

Wata Babbar Kotun Jihar Kano ce ta bayar da umarnin a ranar 5 ga watan Yuni, 2024, inda ta baiwa gwamnatin jihar damar miƙa wa waɗanda ake zargin su bakwai gayyatar, kuma ta aiwatar da hakan ta hanyar wallafa sanarwar a jaridu guda biyu a ranar 6 ga watan Yunin.

Waɗanda ake zargin sune, Abdullahi Umar Ganduje (wanda ake zargi na farko), matarsa Hafsat (wadda ake zargi ta biyu), Abubakar Bawuro (wanda ake zargi na uku), Umar Abadullahi Umar (wanda ake zargi na hudu), Jibrilla Muhammad (wanda ake zargi na biyar), Safari Textiles Ltd. (wanda ake zargi na shida), da kuma Lesage General Enterprises (wanda ake zargi na bakwai).

Alƙaliya Amina Adamu, wadda ke jagorantar kotun, ta bayar da umarnin ne biyo bayan buƙatar hakan daga Zahraddeen Kofar-Mata, lauyan gwamnatin Jihar Kano.