Wani sabon rahoto da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa, NBS, ta fitar ya nuna cewar, jami’an gwamnatin Najeriya sun bayar da cinhancin da ya kai naira biliyan 721 a shekarar 2023 da ta gabata.
Rahoton mai taken ‘Cinhanci a Najeriya: Yanayi da Tsarinsa’, NBS ta sake shi ne a jiya Alhamis.
Hukumar ta ce, an yi ta’ammuli da kuɗaɗen da yawansu ya kai naira biliyan 721 a duk faɗin Najeriya a matsayin cinhanci, abun da ya kai yawan kaso 0.35 na alƙaluman tattalin arziƙin Najeriya na GDP.
Rahoton da aka gina kan binciken da Ofishin Majalissar Ɗinkin Duniya ɓangaren kula da Magunguna da Aikata Laifuka ya gudanar, ya jaddada cewar matsakaicin kuɗin da masu riƙe da ofisoshin gwamnati suka karɓa na cinhanci a bara shine naira 8,284, abun da ke nuni da samun ƙaruwar badaƙalar kan shekarar 2019, inda suka karɓi matsakaicin cinhanci na naira 5,754.