Matimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya bayyana cewar, ƴancin ƙananan hukumomi zai magance matsalolin kuɗaɗe da ke jawo tarnaƙi ga cigaban ilimi a matakin farko a Najeriya.
Shettima ya ƙara da cewa, hukuncin Kotun Ƙoli na kwanan nan da ya bai wa ƙananan hukumomi cikakken ƴancin tasarrufi da kuɗaɗensu zai bunƙasa harkokin ilimi matakin farko a Najeriya.
Mataimakin Shugaban Ƙasar wanda ya kuma yi gargaɗi kan wulaƙanta ƴancin ƙananan hukumomi, ya bayyana hakan ne a wajen taron ƙaddamar da littafi mai taken ‘Navigating the Politics of Universal Education Policies in Nigeria’, wanda tsohon mataimakin gwamnan Jihar Ekiti, Modupe Adelabu ya rubuta aka kuma gabatar a Abuja yau Alhamis.
Shettima ya bayyana cewar, ƴancin ƙananan hukumomi, waɗanda ke da alhakin tafiyar da harkokin ilimi a matakin farko a Najeriya, zai magance matsalolin da ke kawo tarnaƙi wajen cimma manufar gwamnati a harkar ilimi.
Ya ƙara da cewa, sauye-sauyen da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ke ƙirƙirowa zasu magance matsalolin ƙarancin kuɗaɗe da wadatar manufofin da ke kawowa tafiyar ilimi a matakin farko a tarnaki.