Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

ALBASHIN SANATOCI: Ƴansiyasa Na Ƙoƙarin Kai Ƴan Najeriya Bango, In Ji Wani Ɗan Majalissar Amurka

Wani Ɗanmajalissar Amurka haifaffen Najeriya da ke wakiltar Garin Albany a Majalissar Jihar New York, Beroro Efekoro ya bayyana albashi da alawuns da mambobin Majalissar Tarayyar Najeriya ke karɓa a matsayin abin kaico.

Beroro ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki a birnin New York a ranar Alhamis, lokacin da yake magana kan batun ruɗanin da ke tattare da albashi da alawuns da ƴan majalissun tarayya a Najeriya ke biyan kansu.

Zargin cewar mambobin majalissun na yanke wa kansu albashi ya yaɗu ne bayan ziyarar da wasu mambobin Majalissar Wakilai suka kai wa tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo.

A ranar Lahadin da ta gabata ne, Majalissar Dattawa ta musanta maganar zargin cewar ƴan majalissun tarayya ne ke yankewa kansu albashi.

Haka kuma, bayanai da suka fito daga ofishin kula da kuɗaɗen shiga na ƙasa, sun bayyana cewar kowanne sanata a Najeriya na karɓar alawuns da albashin naira miliyan 1.063 a kowanne wata.

Da yake mayar da martani, ɗan majalissar na Amurka, bayanan da hukumar ta fitar kawai jeka na yi ka ne.