Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Yanda Zanga-Zangar #EndBadGovernance Ta Sa Tinubu Ya Kori Shugabannin DSS Da NIA

Dalilan da suka sa tsohon Darakta-Janar na Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS), Yusuf Bichi, da Darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa (NIA), Ahmed Abubakar, suka sauka daga mukamansu sun bayyana.

Wata majiya daga fadar shugaban ƙasa ta shaida wa jaridar PUNCH cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu, sun tambayi tsarin tattara bayanan sirri na wadannan hukumomi biyu, bayan zanga-zangar #EndBadGovernance da ta yi tsanani a wasu jihohin arewa da kuma ƙwace wasu jiragen shugaban ƙasa uku da aka yi a ƙasar Faransa.

An rawaito cewa Bichi ya dauki alhakin rashin samun bayanan sirri game da zanga-zangar, yayin da aka tuhumi Abubakar bisa gazawar NIA wajen samun rahoton ƙwace jiragen sama kafin faruwar lamarin, wanda wani kamfanin kasar Sin mai suna Zhongshan Fucheng Industrial Investment Co. Limited ya yi.

Wata kotu a Faransa ta bayar da umarnin kwace jiragen sama uku na shugaban Najeriya, ciki har da sabon jirgin Airbus da aka saya, sakamakon wata takaddama ta shari’a tsakanin Zhongshan da Gwamnatin Jihar Ogun.

Zanga-zangar #EndBadGovernance, wadda ta fara a ranar 1 ga watan Agusta, ta yi tsanani a jihohin Kano, Gombe, Yobe, Borno da Bauchi, yayin da zanga-zangar a yankin Kudu ta kasance cikin lumana.

A yayin zanga-zangar a wasu jihohin arewa, an lalata gine-ginen gwamnati da masu zaman kansu, yayin da ‘yan daba suka fasa shaguna da tayar da tarzoma, abin da kuma ya jawo sanya dokar hana zirga-zirga a jihohin Kano, Bauchi, Jigawa, Kaduna, Yobe da Filato.

Zanga-zangar ta samo asali ne daga tsananin wahalar da talakawa ke fuskanta sakamakon cire tallafin man fetur, karin kudin wutar lantarki da tsadar rayuwa, da ma sauran matsaloli.

Tsohon shugaban DSS, Bichi, wanda ya fito daga jihar Kano, inda aka yi ta’adi sosai da fasa shaguna, an naɗa shi ne ranar 14 ga watan Satumba, 2018, a lokacin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

Shi kuma tsohon shugaban NIA, Abubakar, wanda ɗan Jihar Katsina ne, shima Buhari ne ya naɗa shi a ranar 10 ga watan Janairu, 2018.

Majiyoyi masu sahihanci sun bayyana cewa Tinubu da Ribadu sun kunyata kan yanda al’amura suka kasance a maganar ƙwace jiragen shugaban ƙasa da kuma zanga-zangar #EndBadGovernance.