Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Gwajin Gado: Kashi 27% Na Maza Ba Su Ne Iyayen Yaran Da Aka Ce Sun Haifa Ba – Rahoto

Wani sabon rahoto daga Smart DNA, wata cibiya da ke gudanar da gwaje-gwajen kwayoyin halitta a Lagos, ya nuna cewa kashi 27% na maza da suka yi gwajin ƙwayoyin halitta ba su ne iyayen yaran da aka ce sun haifa ba.

Rahoton, wanda ya ƙunshi yanayin gwaje-gwajen kwayoyin halitta daga watan Yulin 2023 zuwa watan Yunin 2024, ya kuma nuna karuwar gwaje-gwaje masu alaka da yunƙurin yin hijira daga Najeriya wanda ke nuna cigaba da matsalar kwararewar ƙwararru ƴan Najeriya don neman mafita a ƙasashen waje.

Jihar Lagos ce ta fi yawan masu yin gwaji don ficewa daga Najeriya, inda aka gudanar da kashi 73.1% na dukkan gwaje-gwajen kwayoyin halitta a jihar, wanda ya kara jaddada banbancin tattalin arziki tsakanin yankunan ƙasar nan.

Rahoton ya kuma bayyana cewa ƙabilar Yarbawa ce ta fi yawan gwajin da kashi 53%, sai Ibo da kashi 31.3%, yayin da Hausawa suka kasance kashi 1.2% kacal.

Wadannan bayanai dai sun haifar da manyan tambayoyi masu mahimmanci game da tsarin zamantakewar iyali da kuma yanayin samun damar yin gwajin kwayoyin halitta a Najeriya.

Smart DNA ya jaddada buƙatar ƙarin bincike kan wadannan al’amura da kuma tasirinsu ga al’umma saboda yawan gwajin da ke nuna cewa ba iyaye maza ba su ne mahaifan yaransu ba.