Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Likitoci Sun Janye Yajin Aikin Gargadi, Za Su Koma Aiki Yau

Kungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta umarci mambobinta su koma bakin aiki a ranar Litinin (yau), bayan yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai da mambobinta suka fara saboda sace abokiyar aikinsu, Dr Ganiyat Popoola.

Popoola dai ta yi wata takwas a hannun masu garkuwa da mutane.

Sai dai NARD ta bayyana cewa za ta sake duba jajircewar Gwamnatin Tarayya wajen magance bukatunta a cikin makonni uku masu zuwa.

NARD ta fara yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai a makon da ya gabata don matsa lamba kan ceto Popoola, wata mai rijista a sashen idanu na Cibiyar Idanu ta Kasa da ke Kaduna.

An yi garkuwa da ita ne a ranar 27 ga Disamba, 2023, tare da mijinta da dan uwanta.

Yayin da aka sako mijinta a watan Maris, Popoola da dan uwanta suna nan tsare a hannun masu garkuwa da su.

A ranar Alhamis, Gwamnatin Tarayya ta ce za ta aiwatar da dokar ‘babu aiki, babu albashi’ ga likitocin da ke yajin aiki, yayin da likitocin suka ce wannan barazana ba zata sare musu guiwa ba.

Da yake magana da ƴan jarida a ranar Lahadi, Shugaban NARD, Dr Dele Abdullahi, ya ce, “Mun dakatar da yajin aikin a yanzu. Za mu gana don sake duba ci gaban da gwamnati ta samar a cikin makonni uku masu zuwa.

“Mun dawowa bakin aiki a ranar Litinin, 2 ga Satumba, 2024, da misalin karfe 8 na safe. Dangantakarmu da gwamnati ta inganta kadan. Amma muna fatan za su ci gaba da wannan kyakkyawan mataki da suka dauka.”