Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Nan Da Awa 48 Man Dangote Zai Shiga Gidajen Mai, An Kuma Bayyana Yanda Farashi Zai Kasance

Mamallakin matatar mai da ke Lagos, Aliko Dangote, a yau Talata ya yi bayani kan yanda za a saka farashin fetur da matatarsa mai tace ganga 650,000 a kowace rana zata fara sayarwa.

Dangote ya bayyana cewa da zarar kamfaninsa ya kammala tattaunawa da Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL), za a fara fitar da fetur ɗin zuwa kasuwa.

“Man fetur ɗin mu na iya isa gidajen mai cikin sa’o’i 48 masu zuwa, ya danganta da abun da NNPCL ya tsara,” in ji shi.

Da aka tambaye shi kan farashin fetur ɗin da matatarsa zata fara fitarwa, Dangote ya ce, “Wannan tsari ne wanda Majalisar Zartarwa ta Tarayya zata tsara kuma ta amince ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

“Da zarar an kammala tattaunawa, wanda shi (Tinubu) ke kokarin kammalawa, da zaran mun gama da NNPC, yana iya kasancewa yau, yana iya kasancewa gobe, mu dai mun shirya fitar da man zuwa kasuwa.”

Ya bayyana cewa “wannan rana ce ta murna” ga ‘yan Najeriya kuma ya tabbatar wa dukkan ƴan ƙasa cewa “za ku samu ingantaccen fetur yayin da injunan motocinku za su daɗe suna aiki. Ba za ku fuskanci matsalar injin ba, wanda da yawa daga cikinmu ke fuskanta. Hakan ba zai faru ba kwata-kwata.”