Kungiyar Daliban Najeriya, NANS, ta fitar da sanarwar shirin rufe dukkan manyan biranen Najeriya, daga ranar 15 ga Satumba, 2024.
Zanga-zangar na da nufin nuna rashin amincewa da ƙarin farashin man fetur da kuma zargin rashin kwarewa da ake yi wa Shugaban NNPC, Mele Kyari.
Kungiyar Daliban tana bukatar a gaggauta janye karin farashin man fetur da kuma cire Mele Kyari daga mukaminsa na Shugaban NNPC.
Daliban sun shirya mamaye dukkan manyan birane a ranar 15 ga Satumba, 2024, kuma sun tabbatar da cewa zanga-zangar za ta kasance cikin lumana da kuma bin doka idan mahukuntan NNPC suka ki cika bukatun masu zanga-zangar kafin lokacin.
An aika sanarwar yin zanga-zangar ga hukumomin tsaro daban-daban, ciki har da Hukumar Tsaro ta Civil Defence Corps (NSCDC), Shugaban Tsaro na Kasa, Rundunar Sojojin Najeriya, da dukkan gwamnonin jihohi.