Shugaban makarantar Moshood Abiola Polytechnic, MAPOLY, da ke Abeokuta, Dr. Adeoye Odedeji, ya ce ɗaliban makarantar sun fara samun kuɗi na bashin karatun da suka nema.
Odedeji ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a Abeokuta yayin rantsar da sabbin shugabannin ƙungiyar dalibai (SUG) ta makarantar.
Ya bayyana cewa bashin daga Asusun Bashi na Ilimi na Najeriya, NELFUND, ya zo wa makarantar domin biyan kuɗin makaranta na daliɓan.
Shugaban makarantar ya nuna damuwarsa kan yanda mafi yawan ɗaliban ba su amfana da damar da gwamnatin tarayya ta ba su ba.
Ya yi kira ga ɗaliban da su yi amfani da wannan dama domin samun sauƙin biyan kuɗin makaranta.
Ya ƙara da cewa, daga cikin ɗalibai 81 da suka nema, 26 ne kawai aka tabbatar sun cancanci samun bashin, kuma sun riga sun samu kuɗin biyan kuɗin makarantar.
Odedeji ya tabbatar da cewa za a ci gaba da samun haɗin kai tsakanin shugabancin makarantar da ɗalibai wajen ciyar da makarantar gaba.