Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Tinubu Ya Amince Da Ajjiye Aikin Mai Magana Da Yawunsa, Yai Masa Fatan Alheri

Fadar Shugaban ƙasa ta sanar da karbar takardar ajiye aiki na dindindin daga mai Magana da Yawun Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, Ajuri Ngelale, saboda dalilai na ƙashin kansa da kuma matsalolin lafiyarsa.

Wannan ya bayyana ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a shafin X na Fadar Shugaban Ƙasa @NGRPresident a daren jiya Asabar.

Sanarwar da ba ta ɗauke da sunan wani mutum amma aka sanya hannu da “The Presidency” ta ce an karɓi uzurin Ngelale game da ajiye aikin nasa.

Shugaban Ƙasa ya amince da dalilan da Ngelale ya bayar game da ajiye aikin, kuma ya nuna fahimta da tausayawa ga yanayin da ya kai ga wannan mataki.

Shugaban Ƙasar ya yaba wa Ngelale bisa ƙoƙarinsa da sadaukarwarsa wajen bautawa ƙasa, musamman a fannin inganta harkokin hulɗa da jam’ar ƙasa da jagorantar ayyukan kare muhalli da sauran muhimman ayyuka.

Sanarwar ta kuma yi kira da a mutunta buƙatar Ngelale da iyalinsa na samun nutsuwa yayin wannan lokaci.

Ngelale ya sanar da matsayinsa na yin murabus daga dukkan muƙaman da yake rike da su a Fadar Shugaban Ƙasa saboda dalilai na iyali da kuma rashin lafiyar da ta ƙara ta’azzara masa.

Ya kuma bayyana cewa ya ajiye muƙaminsa na Jakadan Shugaban Ƙasa na Musamman kan Harkokin Kare Muhalli da kuma Shugaban Kwamitin Shirye-shiryen Shugaban Ƙasa na Project Evergreen.