Wata babbar jami’a a Ma’aikatar Harkokin Waje ta Amurka ta ce, Amurka na neman damar ziyartar wani babban jami’in Binance, Tigran Gambaryan, wanda ke tsare a gidan yari na Kuje a Abuja.
Gambaryan, dan kasar Amurka kuma shugaban sashen hana aikata laifukan kudi na Binance, an kama shi ne a watan Fabrairu 2024 tare da wani jami’i, Anjarwalla, yayin da suka iso Najeriya.
An tsare su ne sakamakon binciken da ya danganta Binance da zambar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci.
Mai shari’a Emeka Nwite na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya sanya ranar 9 ga watan Oktoba domin yanke hukunci kan sabon neman beli da lauyoyin Gambaryan suka gabatar.
Binance da iyalan Gambaryan sun nuna damuwa kan yanayin lafiyarsa, suna iƙirarin an hana shi samun isasshiyar kulawar likita da hana shi samun kujera na zama.
Tsohon Jakadan Najeriya a Mexico da Singapore, Ogbole Amedu-Ode, ya ce buƙatar Amurka na samun damar ziyartar Gambaryan tana da tushe, amma bai kamata ya kawo cikas ga tsarin shari’ar Najeriya ba.