Aƙalla sojoji 196 da ke aikin yaki a yankin Arewa maso Gabas da sauran wuraren yaƙi sun rubuta takardun ajiye aiki ga shugaban rundunar sojin ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, don yin ritaya da son ransu.
Matakin na su ya zo ne a lokacin da sojojin Najeriya ke fuskantar matsalolin tsaro da ke ƙara ta’azzara a sassan ƙasar.
Wasu majiyoyi sun bayyana wa SaharaReporters cewa yawancin sojojin da ke barin aikin na neman shiga rundunonin sojin wasu ƙasashe, ciki har da rundunar sojin Birtaniya, Ukraine, da sauran ƙasashen da ke cikin Commonwealth.
Sojojin da ke cikin jerin sun fito daga sassa daban-daban na rundunar sojin ƙasar, kuma dukkan su sojoji ne ƙananan mataimaka.
Shugaban rundunar sojin ƙasa ya amince da ritayar ta su.
Jerin sojojin da suka ajiye aiki bai bambanta tsakanin waɗanda suka yi ritaya don son ransu da kuma waɗanda suka bar aiki bisa dalilan lafiya.
Duk da haka, babu ɗaya daga cikinsu da ya kai shekaru na ritaya.
Amincewar ritayar ta son ransu mai farawa a ranar 23 ga watan Agusta, an sanya hannu a kanta ta hannun Birgediya OH Musa.
An yi zarge-zargen cin hanci a cikin rundunar sojin Najeriya, wanda wasu daga cikin sojojin suka danganta da matsalar tsawaita lokacin zama a yankin Arewa maso Gabas.
Sojoji sun koka da cewa ana tilasta musu yin faɗa da ƴan Boko Haram, suna mai cewa ƙarancin ƙwarin gwiwa da rashin niyyar cigaba da yaƙi ya bai wa ƴan ta’adda damar ƙwace wasu sansanonin soja a kwanan nan.
SaharaReporters ta ruwaito cewa wasu daga cikin sojojin sun nuna sha’awar yin ritaya saboda rashin walwala, ƙarancin kayan aiki, da kuma rashin ƙarfafawa daga ɓangaren rundunar sojin Najeriya.