Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

An Gabatar Da Shugabannin Ƙungiyar ACF Reshen Jigawa

A ranar Asabar da ta gabata ne aka ƙaddamar da kwamitin shugabancin reshen Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa a Jihar Jigawa.

An ƙaddamar da shugabancin domin assasa ƙungiyar a Jihar Jigawa tare da tabbatar da cewa ba a bar jihar a baya ba wajen bayar da gudunmawar cigaban yankin Arewa.

Dattawan da aka ɗorawa wannan nauyi sun haɗa da Ambasada Aminu Dalhatu a matsayin Shugaba, sai Abdullahi Dogo Abubakar a matsayin Mataimakin Shugaba da kuma Abbati Dankanti a matsayin Babban Sakatare.

Sauran shugabannin sun haɗa da Ahmed Garba a matsayin Sakataren Kuɗi, yayin da Group Captain Usman B. Sulaiman ya zama Mataimakin Sakataren Kuɗi da kuma Sani Ahmed Ubandoma a matsayin Ma’aji.

Akwai kuma Alhaji Ali Abdulkadir a matsayin Sakataren Yada Labarai, sai Abubakar S. Addani a matsayin Mataimakin Sakataren Yada Labarai da Hon. Gausu Boyi a matsayin Mai Bayar da Shawara kan Harkokin Shari’a.

Ana sa rana waɗannan dattawa zasu na tattaunawa kan matsalolin al’umma tare da tuntuɓa da nemo musu mafita daga wuraren da suka dace.

Idan za a iya tunawa Ahaji Bashir Dalhatu wanda ɗan asalin Jihar Jigawa ne shugaban Kwamitin Amintattu na Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa a Najeriya.