Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ambaliyar Ruwa Ta Cinye Fadar Shehun Borno, Ta Raba Mutane Da Gidajensu

Ambaliyar ruwa ta mamaye fadar Shehun Borno, Alhaji Garbai Elkanemi, da wasu sassan birnin Maiduguri a farkon safiyar yau Talata, inda hakan ya tilastawa mutane barin gidajensu.

Wani rahoto ya bayyana cewa Shehun Borno ya bar fadarsa zuwa gidan gwamnati domin samun mafaka, sakamakon mamayar ruwan.

Wani mazaunin Kofar Shehu ya bayyana mamakinsa game da wannan lamarin, yana mai cewa, “Ban taba ganin irin wannan ba. Har Shehun ma ya bar fadarsa zuwa gidan gwamnati.”

Rahotanni sun nuna cewa yankunan da suka fi shan wahala a ambaliyar sun hada da titin Lagos, Modugari, Post Office, da Gwange, inda mazauna yankunan ke kokarin ceton kayayyakin su da rayukansu.

Usman Babagana, ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, ya ce sun samu gargaɗi tun da wuri cewa ruwa na tafe, amma mutane basu ɗauki lamarin da muhimmanci ba.