Wata sanarwa daga Gidan Adana Kayan Tarihi na Jihar Borno ta bayyana cewa dabbobin daji masu haɗari sun kutsa cikin unguwannin Maiduguri saboda ambaliyar ruwan da ta mamaye birnin.
Babban Manajan gidan, Ali Abatcha Don Best ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.
Ya ce ambaliyar ruwa ta yi ɓarna sosai ga dukiyoyi tare da kashe fiye da kashi 80 cikin 100 na dabbobin da ke gidan.
Sanarwar ta ce dabbobi masu hatsari kamar kadoji da macizai sun bar gidan tare da kutsawa cikin unguwannin al’umma a dalilin ambaliyar.
Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu ya nuna damuwarsa kan lamarin kuma ya umurci hukumar NEMA da ta taimaka wa waɗanda ambaliyar ta shafa.