Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

TSADAR MAN FETUR: Dillalan Man Fetur Sun Gindaya Sharaɗi Kafin Su Sari Man Ɗangote

Dillalan man fetur a Najeriya sun ce suna cikin ruɗani game da farashin man fetur na matatar Dangote da aka sanar a ranar Litinin ta hannun Kamfanin Man Fetur na Najeriya, NNPCL.

Sun buƙaci matatar Dangote da ta bayyana farashin da ta sayar wa NNPCL don samun ingantaccen bayani na gaskiya.

Sun kuma bayyana cewa Najeriya ba za ta iya dogara da man fetur da ake samarwa a cikin gida wajen biyan buƙatun yau da kullum, wanda ya kai lita miliyan 50 a kowace rana ba, kamar yanda hukumar da ke kula da harkokin man fetur ta kasa ta bayyana.

Shugaban kungiyar masu gidajen man fetur ta PETROAN, Billy Gillis-Harry, da shugaban ƙungiyar masu sayar da man fetur masu zaman kansu, Abubakar Maigandi ne suka bayyana wannan buƙata a wasu hirarraki daban-daban da jaridar DAILY POST a ranar Litinin.

Sun kuma ce, a nan gaba za samu sabon ƙarin farashin man fetur, yayin da NNPCL ya sanar da farashin da zai sayar da man matatar Dangote a gidajen mansa a duk faɗin Najeriya.

A birnin Lagos, farashin zai kai N950.22 kan kowace lita, a Oyo da jihohin kudu maso yamma zai kai N960, yayin da a birnin tarayya Abuja da Kano da Kaduna za a sayar da shi N999.22 kan kowace lita.

A Imo da Ribas, za a sayar da man a N980.2, sai kuma a Borno inda za a sayar da shi kan N1,019.22.

Duk da wannan, NNPCL bai bayyana farashin da zai sayar wa ƴan kasuwa ba, lamarin da ya sanya ƴan kasuwar man jiran bayani don sanin ko za su ci gaba da saye ko kuma su waiwayi shigo da mai daga ƙasashen waje don rufe giɓin da ke akwai.