Kwamitin Daidaita Albashin Ma’aikata ya amince da cewa, sabon mafi ƙarancin albashi zai fara ne daga ranar 29 ga watan Yuli, 2024.
An bayyana hakan ne a takardar yarjejjeniya wadda aka raba a ƙarshen zaman kwamitin yau a Abuja.
Yarjejjeniyar ta ce, kwamitin zai fitar da tsarin albashin da ya dace domin aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin wadda zai fara daga ranar 29 ga watan Yuli, 2024.
An dai samar da wannan kwamiti ne domin aiwatar da Dokar Sabon Mafi Ƙarancin Albashi wadda ta ɗaga mafi ƙarancin albashi daga ₦30,000 zuwa ₦70,000.
Kwamitin dai na da mambobi 16.