Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Babbar Kotun Tarayya Ta Yanke Hukunci Kan Makomar Ganduje A Shugabancin APC

Babbar Kotun Tarayya da ke a Abuja, a yau Litinin, ta ƙi amincewa da cire Dr. Abdullahi Umar Ganduje daga matsayin Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa.

A hukuncin da Mai Shari’a Inyang Ekwo ya yanke, kotun ta yi watsi da ƙarar da Ƙungiyar Ƴan Arewa ta APC ta shigar kan Ganduje, inda ta ce ba ta da inganci.

Kotun ta ce ba a gabatar da wata hujja da ke tabbatar da cewa mai shigar da ƙarar wata ƙungiya ce da a doka ke da ikon shigar da ƙara ba.

Kotun ta ƙara da cewa babu wata shaida da ke nuna an yi wa ƙungiyar rijista bisa ga tsarin dokokin kasa.

Haka kuma, kotun ta ce babu wata shaida da ke nuna cewa ƙungiyar ta yi amfani da hanyoyin sasanta rigingimu na cikin gida na jam’iyya kafin ta garzaya kotu.

Mai Shari’a Ekwo ya kuma ce batun naɗin shugabanni a jam’iyyar APC al’amari ne na cikin gida, wanda ba ya cikin ikon kotu ta shiga ciki.

Kotun ta bayyana cewa ba ta ga wani laifi da ke kan waɗanda ake ƙara ba, don haka ta yi watsi da ƙarar baki daya.

Mai shigar da ƙarar dai ta nemi kotu ta soke naɗin da aka yi wa Ganduje a matsayin Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, tana mai jaddada cewa an yi shi ne saɓanin tanade-tanaden kundin tsarin mulkin APC.