Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Gwamna Namadi Ya Kafa Kwamitin Bincike Kan Tuhumar Da Ake Yi Wa Kwamishinasa

Gwamnatin Jihar Jigawa ta kafa kwamitin bincike don duba tuhume-tuhumen da ake yi wa Kwamishinan Ma’aikatar Ayyuka na Musamman na Jihar, Auwal Danladi Sankara.

Wannan matakin ya biyo bayan rahotannin kafafen watsa labarai da ke danganta kwamishinan da wani rikicin da ya gudana a baya-bayan nan ta hannun Hukumar Hisbah ta Jihar Kano.

A wata sanarwa da aka fitar ranar 19 ga Oktoba 2024, Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya bayyana damuwa kan lamarin, yana mai jaddada cewa wannan tuhuma ta yi mummunan tasiri kan martabar jihar.

“Waɗannan rahotanni sun jawo wa Gwamnatin Jihar jin kunya da koma-baya kan mutuncinta,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, sakamakon haka, gwamantin ta ga ya zama dole ta kafa kwamitin bincike don gano gaskiyar lamarin da tabbatar da sahihancin waɗannan zarge-zarge.

Gwamna Umar Namadi ya naɗa Malam Bala Ibrahim a matsayin shugaban kwamitin, wanda aka ba shi wa’adin makonni biyu don kawo rahotonsa.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da: Kwamishinan Ma’aikatar Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Sagir Musa; Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi Matakin Farko, Lawal Yunusa Danzomo; Mai Ba Gwamna Shawara Kan Harkokin Tsaro da kuma Sakatare na Musamman ga Gwamna, wanda zai kasance Sakatare na kwamitin.

Malam Bala Ibrahim ya yi nuni da cewa kafa wannan kwamitin ya nuna cewa Gwamnatin Jihar na da ƙarfin gwiwa wajen tabbatar da gaskiya da adalci, musamman a lokutan da ake fuskantar matsalolin da za su iya gurbata mutuncinta.

Tuhumar da ake yi wa Sankara ta jawo hankalin jama’a da kuma masu ruwa da tsaki a harkar siyasa.

Ana sa ran binciken da za a gudanar zai kawo cikakken haske kan lamarin, tare da samar da tabbaci ga jama’a da kuma jami’an gwamnati.

Ana sa ran rahoton kwamitin zai fito cikin makonni biyu masu zuwa, bayan kammala binciken da suka yi.