Shugaban kasa Bola Tinubu ya komo Najeriya bayan shafe wasu makonni a cikin hutunsa na shekara a Ƙasar Birtaniya da Faransa.
Jirgin da ya ɗauko Tinubu ya sauƙa a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, da yammacin ranar Asabar, wanda ya kawo ƙarshen ziyarar hutun.
Hadimin shugaban ƙasa Dada Olusegun ya tabbatar da dawowar shugaban ƙasa ta shafinsa na X, inda ya rubuta: “Zaki ya sauƙa. Barka da dawowa, Mr. President.”
Wasu manyan jami’an gwamnati ne suka tarɓi shugaban ƙasar.
Daga cikinsu akwai Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki na Ƙasa, Abdullahi Ganduje; Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu; Shugaban Ma’aikata, Femi Gbajabiamila; da Mai Ba da Shawara Kan Tsaro na Ƙasa, Nuhu Ribadu, da sauransu.
“Ya Huta Sosai Kuma Ya Shirya Don Cigaba Da Aiki”

Gbajabiamila, yayin da yake magana kan dawowar shugaban ƙasar, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnati za ta sake maida hankali wajen daidaita manufofinta bayan dawowar Tinubu.
“Irin aikin da ya gudanar cikin shekara ɗaya da rabi yana buƙatar ɗan hutu. Yanzu ya huta sosai, ya sami sabon kuzari,” in ji Gbajabiamila.
“Yayin hutun yana aiki kuma yana hutu a lokaci guda. Yanzu da ya dawo Najeriya, hankali ya dawo kan aiki, kuma ya shirya don ci gaba.”
Ya ƙara da cewa, “Ƴan Najeriya za su fara ganin tasirin aikinsa. Ya kamata mu kasance masu sa ran kyawawan abubuwa da samar da ƙwarin guiwa, kuma mu rayu da Sabon Fata yayin da shugaban kasa ya dawo Najeriya don ci gaba da ayyukan alherin da yake yi.”
Hutun aiki na makonni biyu na Tinubu ya kasance wani ɓangare na hutun shekara-shekara.
Ya bar Najeriya zuwa Ƙasar Birtaniya ranar 2 ga Oktoba, inda fadar shugaban ƙasa ta bayyana tafiyar a matsayin lokaci na tunani da aiki tun bayan kama shugabanci a watan Mayu na 2023.
Fargaba Kan Jagoranci
Sai dai yayin da yake kasar waje, rahotanni sun bayyana cewa Tinubu ya bar Birtaniya zuwa Faransa, wanda hakan ya samar da damuwa a tsakanin jama’a.
Mai Ba da Shawara na Musamman kan Lamuran Siyasa, Kabir Masari, ya tabbatar da wannan labarin, duk da cewa ba a bayar da dalilin hukuma na canjin wurin ba.
Wannan lamari ya ƙara haifar da damuwa, musamman bayan Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, shima ya bar ƙasar ranar 16 ga Oktoba zuwa Ƙasar Sweden don wata ziyarar kwanaki biyu.
Ya tafi ne don wakiltar Najeriya a tattaunawar diflomasiyya da kasashen Turai.
Wannan rashin kasancewar su biyun a lokaci ɗaya ya jawo muhawara a cikin al’umma, inda fitattun ƴan adawa kamar Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, ya yi tambayoyi game da lamarin.
Obi ya yi amfani da shafinsa na X don bayyana damuwarsa, inda ya ce, “Kodayake yana yiwuwa a ce babu gurbi a fadar shugaban ƙasa duk da rashin shugaban ƙasa da mataimakinsa, amma yana tayar da hankali ga ƙasa da ke fama da matsalolin cikin gida da yawa.”
Fadar Shugaban Ƙasa Ta Musanta Rashin Jagoranci
Duk da damuwar jama’a, fadar shugaban ƙasa ta dage cewa rashin kasancewar shugaban ƙasa da mataimakinsa bai haifar da giɓin jagoranci ba.
Hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa, “Abin lura shi ne, shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa suna ci gaba da kula da al’amuran ƙasa, duk da kasancewar su a waje. Babu giɓin jagoranci a ƙasar.”
Dawowar Tinubu yanzu na nuni da sake mayar da hankali kan shugabanci yayin da gwamnatinsa ke ci gaba da ƙoƙarin magance matsalolin da ƙasar ke fuskanta.