Daga Mika’il Tsoho, Dutse
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, tare da tallafin Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), ta tsara wani gagarumin shiri domin rage adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar da kashi 90 zuwa 95 cikin 100 nan da shekarar 2030.
Da yake jawabi a wajen raba kayan makaranta ga yaran da suka koma makaranta kwanan nan, Shugaban Shirin Ilimi na UNICEF reshen Kano, Mista Macheal Banda, ya jaddada ƙudirin ƴan majalisar Jigawa na magance wannan matsala.
Ya bayyana cewa, ƴan majalisar dokokin Jihar Jigawa da jami’an UNICEF sun gana a Kaduna, inda suka amince su yi ƙoƙarin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta kamar dai yanda Manufofin Ci Gaba Mai Dorewa (SDGs) ya tanada.
“Don tabbatar da ingantaccen ilimi a fannin damar shiga makarantu da koyon karatu, muna nan don ba da goyon baya ga ƴan majalisar dokokin Jigawa. Burinmu shine dawo da kashi 90 zuwa 95 cikin 100 na yaran da ba sa zuwa makaranta zuwa makaranta, sannan a tabbatar sun kai matsayin karatu da adadi kamar yanda SDGs suka tanada kafin shekarar 2030,” in ji Banda.
Ya amince da cewa, Jihar Jigawa tana fuskantar ƙalubale wajen rage yawan yaran da ke ficewa daga makaranta, amma ya nuna fatansa kan samun raguwar hakan.
Banda ya ƙara da cewa, “Tare da ƙudirin jagorancin siyasa na yanzu, da haɗin kan iyaye, al’umma, da sauran masu ruwa da tsaki, za a iya cimma wannan burin,”.
UNICEF, in ji shi, ta kuma fara gudanar da gagarumin kamfen na yaɗa labarai da tattaunawa da masu ruwa da tsaki don neman ƙarin kuɗaɗe.
Waɗannan kuɗaɗe ba kawai za su magance matsalar yaran da ke ficewa daga makaranta ba, za su kuma taimaka wajen shigar da darussa na karatu da lissafi a makarantun koyon Al-Qur’ani.
Da yake magana, Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, Honourable Sani Isyaku Gumel, ya bayyana cewa, yayin taron na su da UNICEF a Kaduna, an bayyana musu cewar akwai fiye da yara 700,000 da ba sa zuwa makaranta a jihar.
Ya ƙara da cewa, sun amince da tsarin rage wannan adadi da kashi 40 a kowacce mazaɓa daga cikin mazaɓun jihar 30.
“A yau, mun ƙaddamar da rabon kayan makaranta ga yaran da suka koma makaranta kwanan nan. Wannan wani ɓangare ne na shirye-shiryenmu da nufin rage adadin yaran da ba sa zuwa makaranta da kashi 40 cikin ɗari a kowace mazaɓa daga cikin mazaɓunmu 30,” in ji Gumel.
A nasa bangaren, Honourable Abubakar Saddiq Jallo, mai wakiltar mazaɓar Hadeja, ya bayyana irin ƙoƙarin da ƴan majalisar ke yi wajen magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta ta hanyar gudanar da kamfe na wayar da kan iyaye, al’umma da masu ruwa da tsaki kan muhimmancin haɗin kai don cimma wannan muhimmin buri.
Ya kuma yabawa UNICEF bisa ci gaba da tallafa wa Jigawa wajen magance matsalolin da yara ke fuskanta, musamman a fannin lafiya da ilimi, tare da kira ga sauran masu ruwa da tsaki da su yi koyi da su domin inganta jihar.