Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Kungiyar Kwallon Kafa Ta Jigawa Golden Star Ta Koma Atisaye Bayan Ragin Matsayin Da Ta Samu

Daga Mika’il Tsoho, Dutse

Bayan shakarar rage matsayi, ƙungiyar ƙwallon kafa ta Jigawa Golden Star ta sake tsara kanta kuma ta koma filin atisaye a ranar Litinin da ta gabata.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ƙungiyar, Kwamared Ibrahim Isyaku, ya sanya wa hannu kuma ya rabawa manema labarai.

Dawowar ƙungiyar ta biyo bayan sa hannun gwamnan jihar, Malam Umar Namadi, ta hannun Kwamishinan Labarai, Wasanni, da Al’adu, Sagir Muhammad, wanda ya taimaka wajen ƙirƙirar sabon shugabancin ƙungiyar.

“Sabon shugabancin ƙungiyar Jigawa Golden Star ya ci gaba da atisaye tun ranar Litinin 21/10/24, kuma ya umarci tsoffin ƴan wasa da su dawo,” in ji sanarwar.

Haka kuma, sanarwar ta tabbatar da cewa sabon shugabancin ya himmatu wajen tabbatar da adalci a zaɓen ƴan wasa, tare da nuna cewa zaɓin zai kasance bisa “inganci, cancanta, da ƙwarewa.”

Sanarwar ta kuma yi kira ga dukkan ƴan wasa da su nuna basira, kyakkyawan hali, da ladabi don cimma burin ɗaukaka ƙungiyar ƙwallon kafa ta jihar zuwa babban mataki.