Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Majalisar Dattijai Zata Fara Tantance Sabbin Ministocin Tinubu A Yau

Masu neman muƙaman ministoci sun fara gabatar da takardunsu a shirye-shiryen tantance su da tabbatar da su a gaban Majalisar Dattijai, wanda za a fara a yau (Talata).

Mai Ba Shugaban Ƙasa Bola Tinubu Shawara Na Musamman Kan Harkokin Majalisar Dattijai, Basheer Lado ne ya bayyana hakan a yammacin Litinin, inda ya ce ana ci gaba da karɓar takardun da ake buƙata daga masu neman muƙaman a matsayin matakin farko na tantancewar Majalisar Dattijai.

Lado ya ce, “Ana sa ran za a tantance da tabbatar da waɗannan sunayen a Majalisar Dattijai kamar yanda sashe na 147 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 (wanda aka yi wa gyara) ya tanada.”

A ranar Alhamis da ta gabata ne, Majalisar Dattijai ta karɓi buƙatar Shugaba Tinubu na tantancewa da tabbatar da ministoci bakwai da yake son naɗawa.

Buƙatar ta fito ne a wata wasiƙa da Shugaban Majalisar Dattijai, Godswill Akpabio, ya karanta a lokacin fara zaman majalisar na ranar.

Sunayen da Shugaba Tinubu ya tura sun haɗa da Dr. Nentawe Yilwatda a matsayin Ministan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci; Muhammadu Maigari Dingyadi a matsayin Ministan Ma’aikata da Ayyuka; Bianca Odinaka Odumegwu-Ojukwu a matsayin Ƙaramar Ministar Harkokin Waje; Dr. Jumoke Oduwole a matsayin Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Samar da Ci gaba; Idi Muktar Maiha a matsayin Ministan Ci gaban Kiwon Dabbobi; Yusuf Abdullahi Ata a matsayin Ƙaramin Ministan Gidaje; da kuma Dr. Suwaiba Said Ahmad a matsayin Ƙaramar Ministan Ilimi.

Shugaba Tinubu ya roƙi Majalisar Dattijai da ta hanzarta duba waɗannan sunayen, domin cike muhimman guraben a gwamnatinsa.

Tun da farko, Shugaban Majalisar Dattijai Akpabio ya miƙa buƙatar Shugaban Ƙasa ga Babban Kwamitin Majalisar domin duba su cikin gaggawa.

Wannan ci gaban na zuwa ne bayan Tinubu ya sauƙe wasu ministoci biyar daga muƙamansu a kwanan nan: Uju-Ken Ohanenye (Harkokin Mata); Lola Ade-John (Yawon Buɗe Ido); Farfesa Tahir Mamman (Ilimi); Abdullahi Muhammad Gwarzo (Gidaje da Ci gaban Birane); da Jamila Bio Ibrahim (Matasa).

Tantancewar Majalisar Dattijai a yau za ta ba da damar farko na duba cancanta da manufofin sabbin ministocin da suka shirya ɗaukar nauyin ayyukan da aka tsara su gudanar.