Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

EFCC Ta Fara Bincike Kan Bidiyon Ɗan Kasar China da Ke Lalata Takardun Naira

Hukumar Yaki da Rashawa da Hana Almundahana (EFCC) ta fara gudanar da bincike kan wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, wanda ake zargin wani ɗan kasar China da lalata takardun naira a Lagos. 

Kakakin EFCC, Dele Oyewale ne ya tabbatar da wannan ci gaba, yana mai cewa, “EFCC tana kan bincike kan wannan batu, tsakani da Allah.” 

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a wata masana’antar da ɗan kasar Chinan ya mallaka, wacce ke kan babbar hanyar Lekki-Epe, lokacin da jami’an gwamnatin Jihar Lagos suka yi yunƙurin rufe masana’antar bisa zargin take dokokin gudanarwa. 

A cikin bidiyon da ke ta yawo a kafafen sada zumunta, an ga ɗan kasar Chinan yana tirjiya ga rufewar, inda ya ciro takardun naira daga jakarsa, ya kuma lalata su yayin da ake cacar baki tsakanin sa da jami’an Jihar Lagos. 

Shaidu sun nuna cewa wasu ma’aikata ƴan Najeriya da ke aiki a masana’antar sun kare ɗan kasar Chinan daga kama shi da jami’an Lagos suka yi yunƙurin yi. 

Cecekucen Jama’a

Bidiyon ya haifar da cecekuce a kafafen sada zumunta, inda ƴan Najeriya da dama suka buƙaci a ɗauki mataki cikin gaggawa kan lamarin. 

Fitaccen ɗan jarida a kafar sada zumunta, Daniel Regha, ya bayyana takaicinsa kan abin da ya faru, inda ya rubuta, “EFCC ya kamata ta kama wannan mutumin kuma ta gurfanar da shi a kotu saboda laifin da ya aikata. Duk da haka, abin damuwa shi ne yadda ake take gaskiya a Najeriya. Idan wannan babban ɗan siyasa ne ko kuma na kusa da shi, to tabbas ba za a dauki mataki ba.” 

Sauran masu amfani da kafafen sada zumunta suma sun yi tir da lamarin. 

Wani mai amfani da kafar sada zumunta mai suna @Qladele ya buƙaci hukunci mai tsauri, yana cewa, “Wannan ɗan kasar China wanda ya raina kuɗin Najeriya a kama shi. A kuma rufe masana’antar har abada. Ya raina mutuncin kasar, ya kamata ya samu hukunci. Har ma da waɗanda suka hana a ɗauki mataki, ya kamata su fuskanci hukunci.” 

Shi ma wani mai suna @PureStanley1 ya yi tsokaci, inda ya ce, “Ka yi tunanin wani ɗan Najeriya ya je China ya lalata kuɗin ƙasar bayan gwamnati ta rufe harkokinsa. Wannan raini ne babba ga Najeriya. Duk da cewa ba na goyon bayan gwamnatin Tinubu, wannan abu ya saɓawa mutuncin kasarmu.” 

Masana shari’a sun bayyana cewa lalata naira laifi ne da ake hukunta shi a ƙarƙashin dokokin Najeriya. 

Lauya Tolu Babaleye ya ce, “Za a iya kama wannan mutum, a gurfanar da shi a kotu, kuma idan aka same shi da laifi, za a yanke masa hukunci bisa saɓawa doka ta lalata takardun kuɗi.” 

Kiraye-kirayen Dole a Ɗauki Mataki

Bidiyon na ci gaba da yaɗuwa a kafafen sada zumunta, yana jawo martani daga mutane da dama da ke neman gwamnati ta yi amfani da doka wajen kare darajar kuɗin ƙasar da kuma mutuncin Najeriya. 

Yayin da EFCC ke ci gaba da bincike, wannan lamari ya sake fito da damuwar jama’a game da yadda ake ɗaukar matakan doka a Najeriya, da kuma yadda baƙi ke nuna rashin girmamawa ga ƙasar.