Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ƙungiyar Jigawa Youth Agenda Ta Kare Minista Badaru Kan Zarge-Zarge Marasa Tushe

Ƙungiyar Jigawa Youth Agenda ta yi watsi da abin da ta kira zarge-zarge marasa tushe da wani rukunin matasa da ake zargin suna wakiltar APC a Jigawa suka yi wa Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar. 

Sanarwar da Shugaban ƙungiyar, Dr. Mujahid Assalafi, ya fitar ta bayyana cewa rukunin da ya yi waɗannan zarge-zarge ba shi da rijista a jam’iyyar APC, kuma ba ya wakiltar matasan jam’iyyar a Jigawa. 

Ƙungiyar ta ce, “Wannan ƙungiya an ƙirƙiro ta ne kawai domin yaɗa jita-jita da kawo rashin jituwa a jam’iyyar APC.” 

A cikin sanarwar, Dr. Assalafi ya bayyana cewa Minista Badaru Abubakar ya nuna ƙwarewa da jajircewa a shugabancinsa tun lokacin da ya kasance Gwamnan Jigawa, har zuwa yanzu a matsayinsa na Ministan Tsaro. 

Ƙungiyar ta yabawa Ministan bisa namijin ƙoƙarinsa wajen samar da tsaro, kafa kawance tare da hukumomin tsaro na duniya, da kuma tallafa wa matasa ta fannonin ilimi, aikin yi, da kuma kasuwanci. 

Ta kuma bayyana cewa Minista Badaru Abubakar yana taka rawar gani wajen tabbatar da haɗin kai a jam’iyyar APC, musamman a Jigawa da ma ƙasa baki ɗaya, wanda ke taimakawa wajen cimma burin jam’iyyar da manufofin gwamnatin Tinubu. 

Ƙungiyar ta Jigawa Youth Agenda ta yi kira ga ƴan Najeriya da su yi watsi da waɗannan zarge-zarge, tana mai cewa an yi su ne don karkatar da hankali daga nasarorin da Ministan ke samarwa. 

Dr. Assalafi ya ƙara da cewa, “Tarihin Minista Muhammad Badaru Abubakar abin alfahari ne ga jihar Jigawa da ma Najeriya baki ɗaya.” 

Ƙungiyar ta kammala da cewa ya zama wajibi ga ƴan Najeriya su goyi bayan ƙoƙarin Minista Badaru wajen gina ƙasa mai ƙarfi da ci gaba.