Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na neman bashin sama da naira tiriliyan 2 (dala biliyan 2.2), bayan kaɗa ƙuri’ar amincewa ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin.
Amincewar ta biyo bayan gabatar da rahoton Kwamitin Majalisar kan Lamunin Cikin Gida da Waje, wanda Sanata Wamakko Magatarkada (APC, Sokoto ta Arewa) ya jagoranta.
Bashin, wanda yake cikin tsarin cin bashi na waje na shugaban ƙasa, an tsara shi ne don rage giɓin kasafin kuɗi na naira tiriliyan 9.7 na shekarar 2024.
Tinubu ya rubutawa Majalisar Dokoki a makon da ya gabata yana neman goyon baya kan sabon bashin da ya haura naira tiriliyan 2 da aka tsara a kasafin kuɗin 2024.
Wannan ci gaba na zuwa ne yayin da Najeriya ke fama da ƙaruwar kuɗaɗen biyan bashin waje.
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana a kwanan nan cewa Gwamnatin Tarayya ta kashe dala biliyan 3.58 wajen biyan bashin waje a watanni tara na farkon shekarar 2024 – ƙaruwar kaso 39.77 idan aka kwatanta da dala biliyan 2.56 a daidai wannan lokaci a shekarar 2023.
Rahoton CBN ya nuna tsananin ƙaruwar kuɗin biyan bashi a wasu watanni.
Biya mafi girma na wata guda ya kai dala miliyan 854.37 a watan Mayu 2024, wanda ya ƙaru da kaso 286.52 idan aka kwatanta da Mayun 2023.
A cikin watan Janairu 2024, an samu ƙarin kaso 398.89 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
Yawan kuɗin biyan bashi, tare da sauyin darajar kuɗin ƙasashen waje, ya janyo damuwa kan ɗorewar tattalin arzikin Najeriya.