Wata mummunar gobarar tankar man fetur a garin Majiya, Jihar Jigawa, ta yi sanadin mutuwar mutum 209 tare da jikkatar wasu 99, bisa ga rahoton da kwamitin binciken gobarar tankar ya gabatar.
Wannan tashin hankali, wanda ya faru a ranar 14 ga Oktoba 2024, ya kuma shafi iyalai 167 tare da lalata kadarori na miliyoyin nairori.
Shugaban kwamitin, Hafizu Inuwa ne ya bayyana waɗannan alƙaluma yayin gabatar da rahoton ga Gwamna Umar Namadi a Dutse.
Rahoton ya gano matsalolin tituna, ciki har da lalacewar birki da ramuka, a matsayin manyan dalilan haɗarin.
Tuƙi da dare, gudun wuce kima, da amfani da kwantenar ƙarfe don kwasar man fetur sun ƙara ta’azzarar ɓarnar.
“Rashin da aka yi na rayuka da dukiya ya yi yawa, kuma ya kamata darussan da muka koya su zama jagora wajen ɗaukar matakan kariya,” in ji Inuwa.
Kwamitin ya bada shawarar inganta tsauraran matakan tsaro ga masu jigilar mai, duba hanyoyi a kai a kai, da kuma kafa wata hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa.
Haka zalika, ya ba da shawarar samar da asibitocin da ke ɗauke da sashen kula da waɗanda suka ƙone da waɗanda suka samu raunukan tashin hankali, tare da shigar da iyalan da lamarin ya shafa a cikin shirin ‘Danmodi Care Programme’ don ba su tallafin jin ƙai.
Gwamna Namadi ya yi alƙawarin aiwatar da shawarwarin, yana mai tabbatar da ƙudirin gwamnatinsa na kare rayukan al’umma.
“Za mu dauki matakan gaggawa don hana irin wannan mummunan abu sake faruwa. Tsaron al’umma shine abin da muka fi bai wa fifiko,” in ji shi.