Bayan shekaru da dama na jinkiri da kasa cika wa’adin farawa, Matatar Mai ta Fatakwal a Najeriya ta sake fara tace ɗanyen mai, inda take aiki da kashi 60% na ƙarfinta, kamar yadda Kamfanin Mai na Ƙasa, NNPCL, ya tabbatar.
Mai magana da yawun NNPCL, Olufemi Soneye ne ya bayyana a ranar Talata cewa matatar tana tace ganga 60,000 na ɗanyen mai a kullum.
Matatar man, wacce ke da jimillar ƙarfin tace ganga 250,000 a rana, tana daga cikin manyan dabarun Najeriya na rage dogaro da shigo da man fetur daga ƙasashen waje.
Fara aiki da wani ɓangare na matatar ya zama babbar nasara, bayan kuskuren da aka sha samu a baya wajen sake farfado da ita.
Soneye ya bayyana wannan ci gaban a matsayin mataki mai kyau ga ɓangaren mai da iskar gas na ƙasa, duk da cewa har yanzu akwai tambayoyi kan lokacin da matatar za ta fara aiki da cikakken ƙarfin ta.
Wannan sake farfaɗo da Matatar Man ta Fatakwal ana sa ran zai rage wasu matsalolin da ke addabar sashen mai na ƙasa, musamman ƙalubalen sarƙaƙiyar samarwa da hauhawar farashin man.