Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Gwamnan Kano Ya Soki Ƙudirin Gyaran Haraji na Tinubu, Ya Ce Zai Jawo Rabuwar Kai

Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya ƙi amincewa da gyaran haraji da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar, yana mai cewa zai tauye haɗin kan ƙasa kuma yanzu ba lokacin da ya dace ai hakan ba ne. 

Da yake magana ta bakin mataimakinsa, Aminu Gwarzo, yayin bikin Sabuwar Shekara a Kano, Yusuf ya nuna rashin amincewa da wannan ƙuduri. 

“Wannan dokar gyaran haraji ba ita ce mafita ga matsalolin tattalin arziƙinmu ba. Jihar Kano ta tsaya tsayin daka kan duk wani tsari da zai shafi jin daɗin al’ummarmu,” in ji shi.

Yusuf ya bayyana yadda ƴan Najeriya ke fama da hauhawar farashin kayayyaki da rashin tsaro, yana mai kira ga gwamnatin tarayya da ta mai da hankali kan yaƙi da talauci da yunwa, musamman a yankin Arewa. 

A wani ɓangare, Asagba na Asaba, Farfesa Epiphany Azinge (SAN), shima ya nuna damuwa kan gyaran harajin. 

Ya buƙaci gwamnati ta fifita gaskiya da riƙon amana a lamuran kuɗi tare da tabbatar da daidaito a tattalin arziƙi kafin aiwatar da sabbin tsare-tsaren harajin.