Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Bello Turji Ya Ƙara Tabbatar Da Barazanar Ta’addancinsa Biyo Bayan Harin Ƴanbindiga a Zamfara

Ƴanbindiga da ake zargin suna biyayya ga jagoran ta’addanci Bello Turji sun sace fasinjoji 10 tare da ƙona motarsu a kan hanyar Ƙaura-Namoda zuwa Shinkafi a Jihar Zamfara.

Wannan hari ya biyo bayan gargaɗin da Turji ya yi na cewa dole ne a saki ɗan uwansa, Baka Wurgi, yana mai cewa zai ɗauki matakan ramuwar gayya idan ba a biya buƙatarsa ba. 

Wani mazaunin yankin, Garba Sani, ya tabbatar da aukuwar harin, yana mai cewa, “Wannan shi ne karo na farko da muka ga ƴanbindiga suna ƙona mota bayan sun sace fasinjoji.” 

Dakarun soji sun yi watsi da barazanar Turji, inda Manjo Janar Edward Buba ya bayyana shi a matsayin “wanda aka riga aka yanke wa hukuncin mutuwa,” tare da yin alƙawarin ɗaukar matakai masu ƙarfi a kan shi da sauran shugabannin ta’addanci a shekarar 2025.