Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Mutum 1 Ya Mutu, Ango Na Kwance Magashiyan Bayan Amarya Ta Zuba Guba A Abincin Biki A Jigawa

Wani bikin aure a Jihar Jigawa ya rikiɗe zuwa masifa bayan da aka zargi amaryar da zubawa abincin da aka yi wa baƙi guba, wanda ya bar angon cikin mawuyacin hali da kuma mutuwar wani baƙo ɗaya. 

Lamarin ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Jahun kuma ya jawo tambayoyi kan dalilin wannan ɗanyen aiki da ake zargin amaryar da aikatawa.

Wasu ganau sun shaida wa PUNCH cewa wata muguwar gaba ce ta sa amaryar ta zuba guba a abincin.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar Ƴan Sandan Jihar, Shi’isu Adam, ya ce, “Mun sami rahoton cewa amarya ta zuba wa abincin da aka yi wa baƙi guba, inda hakan ya sa angon ya shiga mawuyacin hali. An kama mutum biyu da ake zargi da hannu a wannan lamari na zubawa abincin guba a lokacin bikin aure.” 

Adam ya ƙara da cewa waɗanda ake zargin su biyu da aka kama su ne amaryar da wata ƙawarta. 

A halin yanzu suna hannun ƴan sanda inda Sashen Binciken Laifuka ke ci gaba da yi musu tambayoyi. 

“Za mu yi duk mai yiwuwa don tabbatar da cewa an yi adalci,” in ji Adam. 

A cewarsa, dukkan mutanen da suka ci abincin da aka zuba wa gubar an basu magani kuma an sallame su daga asibiti, banda ɗaya da ya rasu. 

Adam ya ƙara da cewa, “Rundunar tana ci gaba da gudanar da bincike kan al’amuran da suka shafi wannan lamari, kuma za mu fitar da ƙarin bayani da zarar mun gama bincike. A yanzu dai, za mu tabbatar wa da jama’a cewa mun fara aiki tuƙuru don gano gaskiyar lamarin. Muna kira ga jama’a da su kasance cikin natsuwa da tabbacin cewa za a yi adalci.” 

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomi ba su bayyana sunayen mamacin, angon da sauran waɗanda abin ya shafa ba.