Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Tinubu Ya Karawa Likitoci Da Ma’aikatan Lafiya Shekarun Aiki

Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da karin shekarun ritaya ga likitoci da ma’aikatan lafiya daga shekaru 60 zuwa 65.

Sakataren yada labarai na kungiyar likitoci ta Najeriya (NMA), Mannir Bature, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba, 5 ga watan Fabrairu, a Legas, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito.

Matakin na Tinubu ya biyo bayan barazanar yajin aiki da kungiyar NMA ta yi sakamakon gazawar gwamnatin tarayya wajen aiwatar da tsarin albashi na CONMESS da kuma cika wasu bukatu da suka jima ba a magance ba.

Likitoci da ma’aikatan lafiya sun dade suna korafi kan karancin albashi, jinkirin da ake samu wajen gyara albashi, da kuma matsalolin jin dadin aiki, wanda ke haddasa hijirar kwararrun lafiya daga kasar.

A baya-bayan nan, kungiyar kwararrun likitoci (MDCAN) ta bayyana cewa a cikin shekaru biyar da suka gabata, likitoci 1,300 sun bar kasar, inda suka bar kasa mai mutane kusan miliyan 220 da likitoci 6,000 kacal.

A halin yanzu, Bature ya ce Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Muhammad Pate, an umurce shi da ya gabatar da amincewar ga Majalissar Zartarwa don kammala tsarin doka.

Bature ya kuma ce an tattauna kan inganta jin dadin ma’aikatan lafiya, ciki har da alawus da sauran hakkoki.

Pate ya tabbatar da cewa kudaden biyan hakkokin da aka tara an tanada kuma za a fara rabawa nan ba da jimawa ba.