Jam’iyyar PDP ta kira tsohon gwamnan Jihar Benue, Samuel Ortom, da sakatarenta na kasa mai matsala, Samuel Anyanwu, gaban kwamitin ladabi.
Shugaban kwamitin, Tom Ikimi, ya bayyana a wata sanarwa cewa, sun kira su ne sakamakon koke da wasu mambobin jam’iyyar suka shigar.
Ikimi ya ce kwamitin zai yi amfani da ikon da ke cikin Sashe na 57(1) na kundin tsarin mulkin PDP domin dawo da zaman lafiya a jam’iyyar.
Ya ce sun samu koke-koke biyar, amma sun dakatar da uku domin ba wa kokarin sulhu da Gwamna Bala Mohammed da sauran gwamnonin PDP suke yi dama.
Kwamitin ya yanke hukuncin kiran su a wani taro da za a yi a ranar Laraba, 12 ga watan Fabrairu, 2025 a Abuja.
Ana zargin Anyanwu da ƙin sauƙa daga muƙamin sakataren PDP duk da shan kaye a zaben gwamnan Jihar Imo, wanda hakan ke kawo rikici a jam’iyyar.
Jam’iyyar ta buƙaci Anyanwu ya bar muƙamin domin bai wa wanda aka naɗa daga yankin kudu maso gabas damar riƙe muƙamin, amma ya ƙi yarda.
A cikin makon da ya gabata, Anyanwu ya rubuta takardar koke ga Sufeto Janar na ƴansanda yana gargaɗi kan ƙoƙarin cire shi daga muƙaminsa.
Kwamitin Ikimi ya jaddada cewa za su tabbatar da ladabi da bin doka a cikin jam’iyyar domin dawo da martabar ta.