Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ministan Ilimi Ya Gabatar Da Sabon Tsarin Karatu Na Najeriya Mai Cike Da Cecekuce

Ministan Ilimi na Najeriya, Dakta Morufu Olatunji Alausa, ya gabatar da sabon shirin da zai sauya tsarin karatun 9-3-4, inda zai sanya matakin SS1 zuwa SS3 a karkashin Hukumar Ilimin Bai Daya (UBEC).

Alausa ya bayyana hakan ne a taron gaggawa na Majalisar Ilimi ta Ƙasa da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis, 6 ga Fabrairu, 2025.

Ya ce shirin zai taimaka wajen inganta harkar ilimi da sauƙaƙa kashe kuɗaɗe.

Sai dai kwamishinonin ilimi na jihohi sun nuna rashin amincewa da shirin, suna masu cewa zai iya kawo cikas ga tsarin ilimi a matakin sakandare.

Wasu na ganin yunƙurin ministan yana da alaƙa da burin siyasa, musamman neman kujerar gwamnan Lagos a nan gaba.

Ana sa ran tattaunawa kan wannan batu zai daɗa zafafa yayin da masu ruwa da tsaki a harkar ilimi ke ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu.