Kwamitin wayar da kan jama’a game da cutar Sankara na Kungiyar Likitoci ta kasa reshen Jihar Sakkwato hadin Gwuiwa da Cibiyar binciken cutar Kansa da Magance ta sun shirya wasu tarukan wayarda kan al’umma daga 3 ga watan Fabrairu zuwa 6 ga watan Fabrairu na shekarar 2025.

Wadannan tarukan dai an shirya su ne domin wayar da kan jama’a akan cutar Sankara da kuma Hanyoyin Magance ta a Najeriya, da kuma wasu Batutuwa da suka shafi Nau’ukan Cutar da Hanyoyin Rigakafi.
Hakama taron yana da zimmar samarda Hanyoyin samarda Rigakafin cutar a Jihar Sakkwato, haka kuma an shiya wata lakca ta musamman ga daliban sakandare domin sanarda su Hanyoyin kamuwa da cutar, alamominta da kuma Hanyoyin Rigakafin ta.

Ta Hanyar fadakar da mutane da Kuma fahimtar da su game da cutar, wannan taron kuma na da manufar inganta Hanyoyin matakan kariya domin rage yawan yaduwar cutar a wanann yankin.
Kungiyar ta kuma yi Kira ga Al’umma da su hada hannu domin yaki da cutar Sankara a Najeriya.