Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

JAMB Ta Bayyana Adadin Ƴan Ƙasa Da Shekara 16 Da Suka Yi Rijista A Bana

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a ta Ƙasa (JAMB) ta bayyana cewa fiye da ɗalibai 11,553 da ke ƙasa da shekara 16 sun yi rijistar jarabawar Unified Tertiary Matriculation Examination (UTME) ta shekarar 2025. 

Shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ne ya bayyana hakan yayin da yake duba cibiyoyin jarrabawar kwamfuta (CBT) a Jihar Legas jiya Juma’a.

Ya ce, a cikin kwanaki 10 da suka gabata, an samu nasarar yi wa ɗalibai 782,027 rijista. 

“Yanzu haka, mun yi wa mutum 782,027 rijista, kuma 11,553 daga cikinsu ƴan ƙasa da shekara 16 ne. Wannan yana nuna cewa tsarin mu na bin diddigin waɗanda ke yin rijista yana aiki yadda ya kamata. Har yanzu ba mu kai rabin adadin da muke tsammani ba, amma da zarar mun kammala makonni biyu, za mu kai sama da miliyan guda,” in ji shi.

Oloyede ya bayyana cewa a ranar Juma’a kadai, an yi wa dalibai 18,813 rijista, ciki har da 443 da ke ƙasa da shekaru 16.

Ya ce, “Mun ƙirƙiri wata sabuwar manhaja da ke iya tantance ɗaliban da su ka yi rijista amma su na ƙasa da shekarun da aka ƙayyade.” 

Ya yi nuni da cewa iyaye da yawa suna matsa wa ƴaƴansu lamba su shiga jami’a da wuri, ko dai saboda son ganin sun cigaba da karatu ko kuma wasu dalilai na daban. 

Game da matsalolin network a tsarin rijista, Oloyede ya ce duk da cewa akwai ɗan jinkiri a wasu wurare, ana ɗaukar matakai don tabbatar da cewa an sauƙaƙa wa ɗalibai yin rijistar ba tare da matsala ba.