Majalisar Wakilai ta Najeriya ta amince da matakin Shugaba Bola Tinubu na dakatar da Gwamnan Jihar Ribas, Simi Fubara, tare da kafa dokar ta-ɓaci a jihar, duk da cewa masana doka da dama sun bayyana cewa hakan ya saɓa wa kundin tsarin mulki.
A yayin zaman da aka yi a yau Alhamis, majalisar ta yanke hukuncin ne ta hanyar ƙuri’ar murya, inda Kakakin Majalisa, Tajudeen Abbas, ya bayyana cewa mambobi 243 ne suka halarci zaman.
Yanzu haka dai an miƙa ƙudirin zuwa Majalisar Dattawa domin samun amincewar ƙarshe.
Tun kafin kaɗa kuri’ar, jaridar Peoples Gazette ta ruwaito cewa wasu manyan jiga-jigan gwamnati sun raba cin hanci ga ƴan majalisar domin su goyi bayan dokar ta-ɓacin, duk da cewa tsarin mulki bai ba wa shugaban ƙasa ikon cire zaɓaɓɓen gwamna ba.