Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Najeriya Za Ta Samar Da Kaso 70% Na Magunguna A Cikin Gida Kafin 2030

Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Ali Pate, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin ƙara yawan samar da magunguna da na’urorin lafiya a cikin gida zuwa kashi 70% kafin shekarar 2030, a ƙarƙashin shirin farfado da darajar harkar samar da lafiya a ƙasa.

Pate ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi, inda ya ce ana kuma sa ran samar da mafiyawan rigakafin da ake amfani da su a Najeriya a cikin gida.

Ya ce, wannan fatan kafa tarihin bai samu ba sai bayan aikin kwamitin shugabancin da shugaban ƙasa ya kafa a watan Nuwambar 2023, karkashin jagorancin Dr. Abdu Mukhtar, wanda ke jan ragamar aikin.

Ministan ya ƙara da cewa gwamnati ta haɗa hannu da Empower School of Health, Geneva, don kafa cibiyar horo a Najeriya mai suna Empower Academy Nigeria, wacce za ta mayar da hankali kan fasahohin samar da magunguna da ingancin su.

Empower Academy Nigeria za ta horar da ma’aikata a fannonin fasahar samar da magunguna, nazarin ƙa’idojin lafiya, da tabbatar da inganci, tare da bayar da takardun shaida tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyi kamar WHO da Africa CDC.

Ya kuma bayyana cewa an samu amincewar sama da sabbin kamfanoni 70 a bangaren ƙera kayan kiwon lafiya, inda ake ci gaba da tattaunawa da manyan masu zuba jari na duniya.

A ƙarshe, Pate ya yabawa wasu ministoci kamar Jumoke Oduole da John Enoh bisa rawar da suka taka wajen samar da wannan sauyi a lafiyar al’umma da ci gaban tattalin arzikin ƙasa.