Wata kotu a garin Saldanha Bay na Afirka ta Kudu ta yanke hukuncin cewa Racquel “Kelly” Smith, wata mata mai shekaru 35, ta siyar da ƴarta mai shekaru shida, Joshlin, da ta ɓace tun watan Fabrairun shekarar 2024.
Alƙalin kotun, Nathan Erasmus, ya ce shaidu daga mutane 35 sun tabbatar da cewa an siyar da Joshlin, ciki har da bayanai daga malaminta da fasto da suka ce uwarta ta gaya musu tun shekarar 2023 cewa tana shirin siyar da ƴar don ta samu kuɗi.
Kotun ta samu Smith da abokin zamanta da wani abokinsu da laifin safarar mutane da kuma satar yara, inda alƙalin ya ce “an yi musanyar Joshlin kamar kaya, kuma akwai bayanai da ke nuna an biya kuɗi ko kuma aƙalla an yi alƙawarin biyan kuɗin.”
Lokacin da aka fara neman Joshlin bayan an yi tunanin ta ɓata, Smith ta samu tausayawar jama’a, inda hotunan ƴarta mai korayen idanu suka yaɗu sosai, kuma ministan wasanni na ƙasar, Gayton McKenzie, ya yi alƙawarin bayar da lada har na rand miliyan guda ga wanda ya samo ta.
Amma daga baya ne shari’ar ta bayyana cewa an siyar da yarinyar ga wani boka da ke sha’awar idanunta da launin fatarta.
An yi zaman kotun a ɗakin taron al’umma inda jama’a suka taru suna zanga-zanga tare da kiran cewa, “Muna son Joshlin muna so mu sake ganinta,” sannan aka sanar da hukuncin wanda ɗumbin mutane suka yi murna da shi.
Kotu ta dakatar da shari’ar don yanke hukuncin da zai iya kaiwa ɗaurin rai-da-rai, yayin da ɗaukacin waɗanda ake zargi ba su tsaya a kotun don su kare kansu ba.