Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Sama Da Mutum Dubu Sun Kamu Da Cutar Amai Da Gudawa A Najeriya, Wasu Sun Mutu, In Ji NCDC

Hukumar NCDC ta bayyana cewa an samu ƙaruwar yaɗuwar cutar amai da gudawa (cholera) a faɗin Najeriya, inda aka rawaito cewa, akwai mutum 1,307 da ake zargi da kamuwa da cutar da kuma mutuwar wasu 34 a jihohi 30 tun daga farkon shekarar 2025, kamar yadda Darakta Janar na hukumar, Dr Jide Idris, ya bayyana a wata ganawa da manema labarai a Abuja yau Juma’a.

Dr Idris ya ce, “a mako na 16 na ƙididdigar cututtuka (wanda ya ƙare a ranar 20 ga Afrilu), an samu mace-mace 34 daga cikin mutum 1,307 da ake zargi da cutar, wanda hakan ke nuna kaso 2.6 na mace-mace cikin yawan masu cutar – adadi da ya ninka wanda muke sa rai na ƙasa da kashi 1 cikin 100.”

Ya bayyana cewa yayin da damina ke ƙaratowa, haɗarin yaɗuwar cutar na ƙaruwa, yana mai cewa sama da unguwanni 1,200 da ke cikin ƙananan hukumomi 176 na cikin haɗarin ambaliya mai tsanani, kuma an gano wasu 2,187 waɗanda ke cikin matsaikacin haɗari.

KARANTA WANNAN: Na Ceto Tsarin Fanshon Jigawa Daga Rugujewa – Gwamna Namadi

Dr Idris ya buƙaci haɗin gwiwa daga ɓangarori da dama musamman a fannin ruwa, tsafta da kula da muhalli (WASH) domin daƙile yaɗuwar cutar, yana cewa, “muna kira ga ɗaukacin ƴan Najeriya da su kasance cikin shiri, su bi hanyoyin samun kariya, su kuma ɗauki matakan rigakafi.”

Ya ce cutar cholera na yaɗuwa ta hanyar cin abinci ko shan ruwa da ya gurɓata da ƙwayar cutar Vibrio Cholerae, musamman a yankuna da babu tsafta ko ingantaccen ruwan sha.

Ya kuma ce NCDC na gudanar da tarurrukan wayar da kai a yankunan Kudu maso Yamma da Arewa maso Yamma, tare da shirin faɗaɗa hakan zuwa sauran sassan ƙasar.

Dr Idris ya ja kunnen gwamnatocin jihohi da su guji ɓoye bayanan cutar, su kuma aiko da jerin sunayen waɗanda ake zargi da kamuwa da cutar a kan lokaci domin sauƙaƙa yaƙi da cutar a faɗin ƙasar nan.