Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Jigawa Ta Fara Yi Wa Alhazai Rigakafi Kafin Tafiya Aikin Hajjin Bana

Gwamnatin Jihar Jigawa ta fara allurar rigakafi ga alhazai da ke shirin tafiya aikin hajjin bana a wani mataki na tabbatar da lafiyar su kafin su tashi zuwa ƙasa mai tsarki.

An ƙaddamar da shirin rigakafin ne a Hadejia, hedkwatar yankin Arewa maso Gabas na jihar, ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar na Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, wanda ya ce, “Rigakafin wani ɓangare ne na shirye-shiryen hajjin 2025, kuma za a ci gaba da gudanar da shi a dukkan ƙananan hukumomi 27.”

A cewar sa, alluran da ake yi sun haɗa da na sanƙarau, shawara (yellow fever) da cutar shan inna, wanda kasashe irin Saudiyya ke buƙata ga kowane baƙo da zai shige su.

KARANTA WANNAN: An Kafa Kwamitin Da Zai Jagoranci Tallafawa Matan Jigawa A Fannin Tattalin Arziƙi

Shugaban cibiyar lafiya matakin farko ta Hadejia, Dr Bala Ismaila, ya bayyana cewa rigakafin na da matuƙar muhimmanci wajen hana yaɗuwar cututtuka a lokacin ibada, inda ya ƙara da cewa, “alhazai su riƙa kai rahoton duk wata matsala da za su fuskanta bayan rigakafin.”

An kuma buƙaci mahajjata da su halarci tarurrukan faɗakarwa na aikin hajji domin samun ilimi kan yadda ake gudanar da ibada da kuma dokokin tafiya.

Gwamnati ta ce shirin rigakafin na daga cikin ƙoƙarinta na tabbatar da kyakkyawan shiri da lafiya ga dukkan mahajjata, tare da bin ƙa’idojin kiwon lafiya na ƙasa da ƙasa.

Ana sa ran za a kammala shirin kafin ranar tashin farko zuwa ƙasa mai tsarki da zai gudana a wannan watan na Mayu.