Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na shirin kammala aikin layin dogo mai tsawon kilomita 284 daga Kano zuwa Maradi wanda zai bi ta Jigawa da Katsina nan da shekarar 2026 domin rage cunkoson hanyoyi da bunƙasa zirga-zirgar kaya da mutane.
Yayin ƙaddamar da cibiyar noma ta zamani da kuma hanya mai tsawon kilomita 24 a Katsina, Tinubu ya ce, “Da zarar aikin ya kammala, zai rage matsin lamba a hanyoyinmu, ya kuma sauƙaƙa sufuri da kasuwanci.”
Ya kuma bayyana cewa gwamnati ta bayar da kwangilar gyaran hanyar Marabar Kankara-Dutsinma-Katsina, da kuma hanyar Zaria-Hunkuyi-Dabai-Kafur-Malumfashi-Dayi-Gidan Mutumdaya.
KARANTA WANNAN: Hukumar FBI Da Ta Hana Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ta Amurka Sun Nemi Ƙarin Kwanaki Kafin Fallasa Bayanan Tinubu
“Mun ƙuduri aniyar kammala waɗannan hanyoyi a kan lokaci,” in ji shugaban ƙasar, yana mai cewa an warware duk wata matsala ta fasaha da taƙaddama da ta janyo tsaiko a aikin hanya tsakanin Kano da Katsina.
Shugaban ya yabawa Gwamna Dikko Radda bisa irin cigaban da yake samu a fannin noma da gine-ginen hanyoyi a jihar Katsina, yana mai cewa, “Gwamnatin tarayya ta ba da injinan banruwa sama da 6,000 domin tallafawa manoman rani.”
Radda ya bayyana cewa jihar ta kashe fiye da Naira biliyan biyu wajen sayen tan 448,000 na takin zamani domin amfanin manoma a 2024.
Ya ƙara da cewa, daga ranar Litinin mai zuwa, za a fara rabon tan 400,000 na takin zamani domin shirin shekarar 2025, tare da ƙarin ma’aikatan noman zamani daga 72 zuwa 778 domin kula da amfanin gona da wayar da kan manoma.