Dakarun rundunar Operation HADIN KAI sun shiga artabu mai tsanani da mayaƙan ƙungiyar ISWAP a garin Buni Gari da ke jihar Yobe, lamarin da ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankin.
A wata gajeriyar sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na X, ta tabbatar da cewa “Sojojin Operation HADIN KAI na fafatawa da ƴan ta’addar ISWAP a Buni Gari, jihar Yobe. Za a samu cikakkun bayanai daga baya.”
Wannan harin ya zo ne yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin murƙushe ragowar ƴan ta da ƙayar baya a Arewa maso Gabas.
KARANTA WANNAN: Tinubu Ya Sa Ranar Da Za A Kammala Aikin Layin Dogo Na Kano-Jigawa-Katsina-Maradi
Masu sharhi kan tsaro sun bayyana cewa wannan sabon hari na nuna cewa har yanzu ISWAP na da ƙarfi a wasu yankuna, duk da cewa gwamnati na iƙirarin samun gagarumar nasara.
Wannan na zuwa ne ƙasa da wata ɗaya bayan rundunar ta kai farmaki a yankin da ke kusa da Buni Gari, inda ta hallaka wasu manyan kwamandoji na ISWAP.
Mazauna yankin sun nemi ƙarin tsaro tare da kiran gwamnati da ta ƙara ƙaimi wajen daƙile barazanar ƴan ta’adda a yankin.