Gwamnatin Ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta bayyana damuwa kan yadda wasu ɓata-gari ke sace kayan gwamnati kamar su bututun ruwa da wayoyin lantarki, lamarin da ke haifar da matsaloli ga ci gaban al’umma.
Shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Dr. Muhammad Uba ne ya bayyana hakan bayan idar da sallar Juma’a a garin Birnin Kudu, inda ya ce za a kira iyaye don tattauna hanyoyin daƙile matsalar.
Ya bayyana cewa “nan bada daɗewa ba, za mu ƙaddamar da wani shiri na bai wa matasa kusan ɗari da hamsin kayan koyon sana’a don rage zaman kashe wando.”
KARANTA WANNAN: Da Iya Lambobin Jikin ATM Ɗinka Ƴandamfara Zasu Sace Maka Kuɗi – Ƴansanda
Shugaban ya kuma buƙaci matasan yankin da su nisanci laifuka tare da gargaɗin cewa “duk wanda aka kama, zai ɗanɗana kuɗarsa.”
A nashi ɓangare, limamin masallacin Izala da ke bayan JIMSO, Ustaz Suleman Datti, ya yaba da matakan da shugaban ƙaramar hukumar ke ɗauka.
Ya ce wannan mataki na zuwa ne a lokacin da jama’a ke buƙatar tsaro da samar da zaman lafiya.
A ƙarshe, gwamnatin ƙaramar hukumar ta buƙaci haɗin kan mazauna yankin wajen kare dukiyar gwamnati.